Home Back

Za A Nuna Zango Na 3 Na Shirin “Labarun Da Xi Jinping Ya Fi Kauna” Da Harshen Kazakhstan A Kafofin Watsa Shirye Shirye Na Kasar

leadership.ng 3 days ago
Za A Nuna Zango Na 3 Na Shirin “Labarun Da Xi Jinping Ya Fi Kauna” Da Harshen Kazakhstan A Kafofin Watsa Shirye Shirye Na Kasar

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron majalisar gudanarwar kungiyar hadin gwiwar Shanghai (SCO) karo na 24 a birnin Astana, da kuma ziyarar aiki a kasar Kazakhstan, za a nuna zango na 3 na shirin bidiyo, mai taken “Labarun da Xi Jinping ya fi kauna” da harshen Kazakhstan, ta kafofin watsa shirye shirye daban daban dake kasar, wanda kafar CMG ta kasar Sin ta tsara, tun daga yau Talata 2 ga watan nan na Yuli.

Shirin bidiyon ya mayar da hankali ne ga nuna yadda ake cimma nasarar bai daya, da kare muhallin halittu, da al’adun gargajiya, da mabanbantan al’adu da sauran muhimman batutuwa, kana zai nunawa masu kallo tushen al’adun kasar Sin na turbar zamanantar da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

People are also reading