Home Back

Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Yadda Gwamnatin Tinubu Za Ta Yi Nasara

legit.ng 2024/5/12
  • Femi Adesina ya bayyana yadda ƴan Najeriya za su taimakawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu wajen samun nasara
  • Tsohon hadimin na Muhammadu Buhari, a wani taron da aka gudanar a Legas, ya ba da tabbacin samun ingantacciyar Najeriya nan gaba
  • Adesina ya yi kira da a marawa gwamnatin Tinubu baya, inda ya roƙi ƴan ƙasar da su yi addu’a da fatan alheri ga gwamnati mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Femi Adesina, mai baiwa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce dole ƴan Najeriya su yi iya ƙoƙarinsu don ganin ƙasar nan ta gyaru.

Femi Adesina ya bayyana hakanne a wata tattaunawa da ya yi da hukumar dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas, a ranar Litinin, 25 ga watan Maris 2024.

Femi Adesina ya shawarci 'yan Najeriya
Femi Adesina ya bukaci a marawa Tinubu baya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Femi Adesina Asali: Facebook

Me Adesina ya ce kan gwamnatin Tinubu?

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, mai taimakawa tsohon shugaban ƙasan ya tabbatar da cewa Najeriya za ta daidaita kuma komai zai gyaru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Saƙona ga Najeriya a wannan lokacin shi ne kada a gaza, abubuwa za su gyaru.
"Ƙasarmu ce, ba mu da wata ƙasar. Saboda haka dole ne mu tabbatar ta gyaru domin duk inda muka je ba mu da cikakken ƴancin zama ƴan ƙasa. Najeriya za ta gyaru, za mu zo wurin."

Da yake ci gaba da bayani, Adesina ya ce dole ne a haɗa hannu domin ƙasar nan ta samu ci gaban da ya dace.

Ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

A cewarsa:

"Don haka, mu marawa gwamnati baya, mu yi mata addu'a kuma mu kasance da kyakkyawar niyya ga gwamnati."

Tallafin N50,000: Gwamnatin Tinubu ta yi bayani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatar masana’antu da harkokin kasuwanci ta bukaci wadanda suka cika tallafin Gwamnatin Tarayya da su fara duba sakwanni a wayoyinsu.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris inda ta ce za a tura sakon ne daga FGGRANTLOAN.

Asali: Legit.ng

People are also reading