Home Back

Matar Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ta Rasu

leadership.ng 2 days ago
Matar Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ta Rasu

Hajiya Zainab Garba, matar mataimakin gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba, ta rasu.

Ta rasu ne a ranar Talata a wani asibiti da ke Minna bayan ta yi fama da gajeriyar jinya.

A cikin sakon ta’aziyyar da babban sakataren yada labarun gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ya fitar, ya yi alhinin rasuwarta, inda ya bayyana hakan a matsayin babban rashi ga jihar.

Gwamna Bago, ya yi addu’ar Allah ya jikanta da kuma fatan Allah ya sa Jannatul-Firdaus ce makomarta.

People are also reading