Home Back

MULKIN NAJERIYA: APC da PDP sun gaza, yanzu NNPP ce kaɗai jirgin tsira – Kwankwaso

premiumtimesng.com 2024/5/7
Binta Sipikin, kakakin Kwankwaso ta koma APC
Kwankwaso Rabiu

Ɗan takarar jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana cewa a yanzu dai zaɓin da ya rage wa ‘yan Najeriya shi ne su rungumi NNPP, domin an gwada APC da PDP, kuma duk sun gaza.

Kwankwaso ya furta haka a Abuja, yayin da yake tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta NNPP.

Ya ce NNPP jam’iyya ce mai hangen nesa da karsashin kishin ƙasa, wadda ba za ta taɓa maimaita kurakuran baya da na yanzu da PDP ta tafka da waɗanda APC ke tafkawa ba.

Kwankwaso, wanda ya yi Gwamnan Jihar Kano shekaru takwas, ya ce APC da PDP sun gaza, yanzu NNPP ce kaɗai jirgin tsira.

Dangane da barin matsalar tsaro kuwa, ya ce Sojojin Najeriya za su iya daƙile matsalolin tsaro, amma sai gwamnatin tarayya da ‘yan Najeriya sun ƙara hoɓɓasa.

Tsohon Ministan Tsaro, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana cewa sojojin Najeriya zarata ne, kuma za su iya magance matsalolin tsaron da ke addabar ƙasar nan, amma fa sai an ƙara masu ƙwarin guiwa sosai.

Kwankwaso wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, bayan kammala taron Majalisar Zartaswar NNPP, a Abuja.

Ya ce duk da dai haƙƙin gwamnatin tarayya ne samar da tsaro a cikin ƙasa, to su ma fa ɗaukacin ‘yan Najeriya su na da muhimmiyar rawar takawa, ta hanyar bai wa jami’an tsaro bayanai yadda za su samu nasarorin daƙile ɓatagari.

“A matsayi na na tsohon Ministan Tsaro, kuma tsohon Gwamnan Kano tsawon shekaru takwas, kuma ina da gogewar siyasa, to na yi amanna cewa matsalar tsaro a wuyan gwamnatin tarayya ta ke.

“Mun ga jihohi na ta kafa ƙungiyoyin ‘yan sa-kai da bijilante-bijilante. Wasu lokutan sai dariya ta kama mutum. Saboda maganar gaskiya halin matsalar tsaron da ake fama da ita yanzu a ƙasar, ba wani ko wasu gungun jami’an tsaron da za su iya magance matsalar sai sojoji.”

“Wasun mu da muka taso daga cikin karkara da garuruwa, za su iya tunawa yadda manoma ke tururuwar zuwa gonakin su. To yanzu noman ba ya yiwuwa a yankuna da dama. Ka je gona a kama ka. A biyo ka gida a kama ka. Mun ga yadda raba mutanen karkara da na cikin garuruwa da gidajen su. Wannan babban ƙalubale ne.”

Da ya koma kan batun siyasa, Kwankwaso ya ce APC da PDP duk sun kasa, don haka abin da ya fi wa ‘yan Najeriya shi ne su rungumi NNPP, jirgin tsira, wanda ba ya tangaɗi ballantana ya yi tangal-tangal.

People are also reading