Home Back

Chelsea za ta ɗauki Dewsbury daga Leicester City

bbc.com 5 days ago
 Kiernan Dewsbury-Hall.

Asalin hoton, Getty Images

Leicester City ta sallama tayin £30m da Chelsea ta yi, domin sayen Kiernan Dewsbury-Hall.

Mai shekara 25 na daf da zuwa Stamford Bridge domin a auna koshin lafiyarsa, daga nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida da za ta kare a karshen 2030.

Ɗan ƙwallon bai yadda ya koma Brighton ba a makon jiya, bayan da ƙungiyar ta yi yunkurin sayensa.

Tun farko Leicester City ta bukaci sayen ɗan wasan kan £40m, bayan da ba ta sallama tayin da Chelsea ta fara yi ba.

Haka kuma Leicester City na tattaunawa da Chelsea, domin ɗaukar matashi mai shekara 18, Michael Golding.

Idan Dewsbury-Hall ya kammala komawa Chelsea zai taka leda karkashin Enzo Maresca, wanda ya kai Leicester City Premier, bayan lashe kofin Championship.

Dewsbury-Hall ya ci ƙwallo 12 ya bayar da 14 aka zura a raga a karawa 44 a Championship a kakar da ta wuce.

Hakan ya sa aka bayyana shi a matakin fitatcen ɗan ƙwallon Chelsea a gasar.

People are also reading