Home Back

Ina Da Burin Ganin Mata Sun Dogara Da Kansu A Harkokin Rayuwa – Lu’ayyat Mu’az

leadership.ng 2024/4/29
Ina Da Burin Ganin Mata Sun Dogara Da Kansu A Harkokin Rayuwa – Lu’ayyat Mu’az

Da Farko Za Mu So Ki Bayyana Mana Sunanki?

Sunana Luayyat Mu’az Assadik,Daga garin Kano.

Ko Malamar Nada Aure?

Bani da Aure.

Wanne Sana’a Kike Yi Ahalin Yanzu?

Ina sana’ar sai da yadin hijab dana abaya sannan kuma muna dinkawa.

Mene ne Ya Baki Sha’awar Fara Wannan Sana’ar?

Saboda shi zama haka baze yiwu ba duk me son ya tsira da mutunchinsa dole sai ya nemi na kansa,musamman wannan zamani da muke ciki na tsdan rayuwa.

Idan Mutun Na Son Fara Wannan Sana’ar Wani Abu Zai Tanada Don Samun Cikakkiyar Nasara?

Abu na Farko gaskiya Shine JARI saboda sana’a sai de jari,musamman wannan Sana’ar na Saida hijabai.

Tayaya Kike Tallata Hajojinki?

Ina tallata haja ta online platforms da kuma wuraren haduwa kaman gidan biki ko suna da makaranta sannan nakan Dinka nasa a jikina ta yadda wasu zasu gani Idan ya musu kyau sai ace na dinka kalan su.

Ko Kin Taba Samun Tallafin Gwamnati Ko Wata Hukumar a Harkar Kasuwanci?

A’a gaskiya.

Ko Zaki Bayyanamana Wani abun daya taba Faruwa dake na Farin ciki ko akasin haka a rayuwarki na wannan Sana’ar?

Toh duk bangaren biyun ba za’a rasa bah amma ina jin dadi sosai idan na tura kaya ya isa hannun masu shi kuma suka yaba hakan na faranta min sosai.

Wanne shawara kike da shi ga al’umma?

Shawara na shi ne gaskiya al’umma su dage abar zaman banza kowa ya nemi na kanshi Saboda wannan yanayin da muke ciki zama haka bashi da wani fa’ida musamman ma yanuwana mata a dena dogaro a wurin maza 100%, Sannan kodan mu taimake iyayan mu da yan’uwa.

Ya kike ganin yanayin tarbiya a wannan lokacin?

Toh! Gaskiya al’amarin tarbiyya sai godia, iyaye sai sun kara sanya ido akan yara sannan kuma adena sakaci da addu’a domin Allah ne me shiryarwa.

Mene ne burinki a wannan sana’ar taki?

Alhamdulillah ni dai ina da burin inga ana damawa da yanuwana mata a kowanne fanni idan Allah ya kara habbaka min ina da burin in tallafi rayuwan mata yanuwana saboda ya zama andaina barinmu a baya,ya zama suma su dogara da kansu.

 
People are also reading