Home Back

Mawaƙan ƴan mata da ke bijire wa Taliban

bbc.com 2024/5/17

Asalin hoton, Kawoon Khamoosh

Afghanistan
Bayanan hoto, 'Yan matan sun shahara ne a shafukan sada zumunta. A nan, suna bidiyon daya daga cicin wakokinsu.
  • Marubuci, Kawoon Khamoosh
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,
  • Mintuna 6 da suka wuce

Yayin da duniya ke kallon yadda gwamnatin Taliban ta koma kan karagar mulki a watan Agustan 2021, wasu 'yan'uwa mata biyu a Kabul na cikin miliyoyin mata a Afganistan wadanda suke fuskanta matsin wannan sabuwar gwamnatin.

Sun yanke shawarar ba za su iya tsayawa kawai suna kallo ba, haka ya sa suka fara amfani da muryoyinsu a asirce don su bijirewa gwamnatin.

Duk da cewa sun jefa kansu cikin babban hatsari, sun fara wani yunkuri na rera waka a shafukan sada zumunta da aka fi sani da Last Torch.

"Za mu rera wannan wakar amma zai iya zama sanadiyyar mutuwarmu," in ji daya daga cikinsu a wani bidiyo da aka dauka kafin su fara wakar.

An sake bidiyon a watan Agustan 2021, 'yan kwanaki bayan da Taliban sun karbi mulki, kuma yadu a Facebook da WhatsApp.

Ba tare da amfani da na'urar kade-kade ba, ’yan uwa mata - wadanda suke sanya niqabi don boye kansu - sun shahara a fannin wake-wake.

"Fafutukarmu ya fara ne tun daga karkashin tutar Taliban da kuma 'yan Taliban," in ji Shaqayeq (ba sunanta na gaskiya ba), karamar 'yar kungiyar.

"Kafin Taliban ta hau mulki, ba mu taba rubuta waka ko daya ba, abin da Taliban suka yi mana ke nan."

Asalin hoton, Last Torch

 Taliban
Bayanan hoto, Wasu mata sanye da hijabi

Bayan ta koma kan karagar mulki, kungiyar Taliban ta dauki kwanaki 20 don aiwatar da manufofinta na musamman kan Afghanistan.

Ta dora dokar Shari'a (Dokar Addinin Musulunci) a harkokin yau da kullum, hana mata damar samun ilimi na daga cikin abubuwan da suka sa a gaba. Mata sun fito kan titunan birnin Kabul da sauran manyan biranen kasar domin nuna adawa da matakan, amma sun fuskanci mumunar murkushewa.

"Mata su ne fata na karshe da mu ke gani," in ji Shaqayeq.

"Don haka ne muka yanke shawarar ci gaba da fafutukarmu inda muka sanya wa kungiyarmu suna Last Torch, muna tunanin ba za mu iya zuwa ko'ina ba, sai muka yanke shawarar fara wata zanga-zanga a asirce daga gida."

Ba da daɗewa ba 'yan uwan su ka saki wasu waƙoƙin, waɗanda aka rera sanye da niqabi, kamar yadda suka rera waƙar farkon.

Daya ita ce shahararriyar waka ta marigayiya Nadia Anjuman, wacce ta rubuta wakar domin nuna adawa da kwace mulkin da Taliban ta yi a karon farko a shekarar 1996.

Yaya zan iya maganar zuma alhalin bakina ya cika da guba?

Kaico, a fasa min baki…

Oh wata rana zan karya keji,

In fita daga wannan kejin kuma na raira waƙa cikin farin ciki.

Asalin hoton, Haroon Sabawoon/Anadolu/Getty Images

Zanga zanga
Bayanan hoto, Wasu matan Afghanistan

Yayin da kungiyar Taliban ta haramta karatun mata, Nadia Anjuman da kawayenta sun kasance suna haduwa a wata makarantar boye mai suna The Golden Needle, inda suke yi kamar suna dinki amma sai suna karanta littattafai. Su ma sun sanya niqabi mai kalar shudi, wanda aka fi sani da chadari a Afghanistan.

Babbar cikin mata biyun mawaƙa, Mashal (ba ainihin sunan ta ba kenan), ta kwatanta nikabin da “’ kejin wayar hannu”.

"Kamar makabarta ce da ake binne fatan dubban mata da 'yan mata," in ji ta.

Shaqayeq ta kara da cewa "Wannan niqabin kamar dutse ne da 'yan Taliban suka jefawa mata shekaru 25 da suka gabata. “Kuma sun sake yin hakan a lokacin da suka koma kan mulki.

"Mun so ne mu yi amfani da makamin da suka yi amfani da su wajen yakar mu, domin mu yi yake takunkumansu."

Daya daga cikin matan
Bayanan hoto, 'Yan matan na amfani da niqabin don boye kansu.

Zuwa yanzu dai ‘yan’uwan sun fitar da wakoki bakwai ne kawai amma kowacce ta yi kakkausar...ga mata a fadin kasar. Da farko sun yi amfani da kalmomin wasu marubuta, amma sun kai matsayin da "babu wata waka da za ta iya bayyana yadda muke ji," in ji Shakyeq, don haka suka fara rubuta nasu.

Jigogin su shi ne takunkuman da aka sanya a kan rayuwar mata ta yau da kullun, daure masu fafutuka da kuma take hakkin dan adam.

Magoya bayansu sun mayar da martani ta hanyar sanya nasu wakokin a shafukan sada zumunta. A wasu lokuta kuma sun sanya niqabi a a matsayin boye kansu, yayin da wani rukuni na daliban makaranta 'yan Afganistan da ke zaune a kasar waje suka rubuta wani siga a dakin taro na makarantar.

Wannan shi ne akasin abin da Taliban ke son cimmawa.

Daya daga cikin matakan farko da ta dauka bayan karbar mulki shi ne maye gurbin ma'aikatar harkokin mata da ma'aikatar yada kyawawan dabi'u da kuma dakile abubuwa al fasha. Sabuwar ma'aikatar ba tilasta sanya niqabi kadai ta yi ba, har ma ta yi Allah wadai da kade-kade bisa zargin lalata tushen Musulunci.

Sawabgul, wani jami’in da ya bayyana a daya daga cikin faifan bidiyo na farfaganda na ma’aikatar ya ce, “Waka da sauraron kade-kade na da illa matuka. "Yana shagaltar da mutane daga hanyar Allah... kowa ya nisance ta."

Ba da dadewa ba sai ga bidiyon sojojin kafa na Taliban a shafukan sada zumunta, suna kona kayan kide-kide tare da nuna mawakan da aka kama.

Asalin hoton, Bakhter News Agency

Mayakan Taliban
Bayanan hoto, Mayakan Taliban na kona wasu kayayyaki

Shaqayeq ta ce ta sha kwana da yawa babu barci tana tunanin Taliban za ta iya gane su.

"Mun ga barazanarsu a shafukan sada zumunta: 'Da zarar mun same ku, mun san yadda za ku cire harshen ku daga makogwaro," in ji Mashal.

"Iyayenmu suna jin tsoro a duk lokacin da suka karanta waɗannan maganganun, suna cewa watakila ya isa kuma mu daina... Amma muna gaya musu ba za mu iya ba, ba za mu iya ci gaba da rayuwarmu ta yau da kullun ba."

Domin tsaron su ‘yan’uwan sun bar kasar a bara amma suna fatan dawowa nan ba da dadewa ba.

Afghanistan
Bayanan hoto, A kan tituna, mata sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin da Taliban ta dauka na hana ilimi - tare da yada hotunan zanga-zangar ta a shafukan sada zumunta

Sonita Alizada, kwararriyar mawakiyar rap ce daga Afghanistan a yanzu tana zaune a Kanada, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka yaba da bidiyon Last Torch.

"Lokacin da na ga wasu mata biyu a sanye da niqabi suna waƙa, gaskiya sai da na yi kuka," in ji ta.

An haife ta a shekarar 1996, shekarar da Taliban ta fara mulkin kasar, kuma danginta sun gudu zuwa Iran tun tana karama. A can mahaifiyarta ta yi ƙoƙari ta sayar da ita don auren dole, amma ta sami hanyar fita ta hanyar kiɗa. Kamar ’yan’uwan biyu na Last Torch, tana ganin matan da suka yi zanga-zangar adawa da Taliban a matsayin fata mai kyau.

Daya daga cikin wakokin ‘yan uwa na yi wa masu zanga-zangar kai tsaye.

Yaƙinku yana da kyau. Mata kukan ku.

You are my broken picture in the window.

......................

"The situation is very disappointing in Afghanistan right now because we have lost decades of progress," Sonita says. "But in this darkness there's a light still burning. We see individuals fighting with their own talent."

"Halin da ake ciki yana da matukar takaici a Afghanistan a yanzu saboda mun yi asarar ci gaban shekaru da dama," in ji Sonita. "Amma a cikin wannan duhun akwai haske har yanzu yana ci. Muna ganin daidaikun mutane suna fafutuka ta hanyar amfani da basirar da Allah ya basu."

Farida Mahwash
Bayanan hoto, Farida Mahwash

The BBC also showed one of the sisters' most recent songs to Farida Mahwash, one of Afghanistan's most celebrated female singers, with a career of over half a century until her recent retirement.

BBC ta kuma nuna daya daga cikin wakokin 'yan uwa na baya-bayan nan ga Farida Mahwash, daya daga cikin mawakan mata da suka yi fice a kasar Afganistan, wadda ta shafe sama da rabin karni tana aikinta har zuwa lokacin da ta yi ritaya a baya-bayan nan.

"These two singers will turn four and then become 10, and then 1,000," she said. "If one day they go on stage, I'll walk with them even if I have to use a walking stick."

“Wadannan mawakan biyu za su zama hudu sannan su zama 10, sannan su 1,000,” inji ta. "Idan wata rana suka hau kan dandamali, zan yi tafiya tare da su ko da zan yi amfani da sandar tafiya ce."

In Kabul, the crackdown on activism has further intensified in the past year, with authorities banning women from holding rallies and arresting those who defy the ban.

A birnin Kabul kuma, a cikin shekarar da ta gabata an kara tsananta takunkumai na kan masu fafutuka, inda hukumomi suka haramta wa mata gudanar da taro tare da kame wadanda suka bijirewa dokar.

One of the sisters' latest songs is about female activists who were imprisoned by the Taliban and kept in what Human Rights Watch described as "abusive conditions".

Daya daga cikin sabbin wakokin 'yan uwan ​​game da mata masu fafutuka ne da 'yan Taliban suka daure kuma aka ajiye a cikin abin da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta bayyana a matsayin "na cin zarafi".

The waves of female voices

break locks and chains of prison.

This pen filled with our blood

breaks your swords and arrows.

Taguwar muryar mata

na karya makullai da sarkokin gidan yari.

Wannan alkalami cike da jininmu

na karya takuba da kibiyoyi.

"These poems are just a small part of the grief and pain we have in our hearts," Shaqayeq says.

"Wadannan wakokin kadan ne daga cikin bakin ciki da radadin da muke ji a zukatanmu," in ji Shaqayeq.

"The pain and struggle of the people of Afghanistan, and the grief they have endured under the Taliban in the last years, can't fit in any poem."

"Ciwo da gwagwarmayar da mutanen Afganistan su ke fuskanta, da kuma bakin cikin da suka sha a karkashin 'yan Taliban a shekarun baya, ba za su dace da kowace waka ba."

The UN says the Taliban could be responsible for gender apartheid if it continues with its current policies. The Taliban has responded that it is implementing Sharia, and won't accept outside interference in the country's internal affairs.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce responsibility din nuna wariyar jinsi za ta iya fadawa a kan Taliban idan ta ci gaba da manufofinta na yanzu. Taliban ta mayar da martani da cewa tana aiwatar da Shari'a, kuma ba za ta amince da tsoma baki daga waje a cikin harkokin cikin gidan kasar ba.

Shaqayeq and Mashal are working on their next songs. They are hoping to echo the voice of women in Afghanistan in their fight for freedom and the right to study and work.

Shaqayeq da Mashal suna aiki a kan wakokin su na gaba. Suna fatan inganta muryoyin mata a Afganistan a yakin neman 'yanci da 'yancin yin karatu da aiki.

"Our voice won't be silenced. We are not tired. It's just the beginning of our fight."

"Ba za a toshe mana baki ba, ba mu gaji ba, yanzu muka fara."

The sisters' names have been changed for their safety.

An canza sunayen ’yan’uwan don kare su.

BBC 100 Women
Bayanan hoto, Mata 100
People are also reading