Home Back

An dakatar da magoya bayan Ingila shida kallon wasannin Euro 2024

bbc.com 6 days ago

Asalin hoton, Getty Images

'Yansandan Birtaniya na harkokin ƙwallon ƙafa kan yi aiki tare da na Jamus a gasar Euro 2024
Bayanan hoto, 'Yansandan Birtaniya na harkokin ƙwallon ƙafa kan yi aiki tare da na Jamus a gasar Euro 2024

Mintuna 5 da suka wuce

Hukumomi sun dakatar da magoya bayan Ingila shida daga shiga kallon wasanni sakamakon rashin ɗa'a da suka nuna kafin fara gasar Euro 2024 a wasa da Serbia.

Mutanen da aka hukunta ba za su iya shiga kallon wasa ba a gida da kuma wajen Ingila har zuwa ƙarshen wa'adin hukuncin.

Shugaban tawagar 'yansandan Birtaniya ta UKFPU, Mick Johnson, ya yaba wa "matakin cikin hanzari" kuma ya ce hakan ya nuna "akwai hukunci" kan duk wanda ya tayar da fitina a Birtaniya ko kuma wata ƙasa.

"Muna ci gaba da aiki tare da abokan aikinmu na Jamus kuma muna da rundunar da muka tura domin taimaka masu wajen gudanar da gasar cikin kwanciyar hankali," in ji Johnson.

An dakatar da Todd Hines, mai shekara 21, da Liam Jackson mai 28, da Kyran Alcock mai 28 tsawon shekara uku, yayin da aka dakatar da ewis Dodsworth mai shekara 29, da Jack Hatton mai 27, da Gary McIvor mai 38 shekara biyar.

Tuni wasu magoya bayan suka gurfana a gaban kotu a Birtaniya kuma aka ba da belinsu kan sharaɗin sai sun bayar da fasfonsu.

'Yansandan UKFPU na ci gaba da bincike kan wasu magoya da ake zargi da hatsaniya kafin wasan da Ingilar ta tashi 1-1 da Serbia.

People are also reading