Kano: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau ya Raba Motoci 107 a Mazabarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano-Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya rabawa 'yan mazabarsa tallafin motocin sufuri 107.
Sanata Barau, wanda shi ne Mataimakin Shugaban majalisar kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) na farko kuma mukaddashin shugabanta a yanzu ya raba motocin ne ranar Litinin.
The Guardian ta wallafa cewa Sanatan na da yakinin motocin za su taimaka wajen saukaka zirga-zirga ga al'ummar Kano baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Direbobin kungiyar Kula da Motocin Haya ta NURTW ne suka yi nasarar sayen motoci a tsarin biya a hankali, kuma a farashi mai sauki kamar yadda suka bayyana.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa an raba motocin ne ga wadanda Sanata Barau ke wakilta, wato Kano ta Arewa.
Daya daga mambobin kungiyar, Malam Rabi’u Bichi da ya rabauta da motar ya ce hakan zai taimaka musu sosai.
Ya ce wannan zai saukaka zirga-zirga sosai a mazabar da ma sauran sassan jihar. Sannan ya yaba da yadda Sanatan ke kawo musu ayyukan ci gaba da saukaka rayuwa.
A madadin sauran wadanda suka samu motocin, Malam Rabi'u Bichi ya yiwa Sanata Barau addu'ar ci gaba da alkhairi ga mutanensa.
A baya mun ba ku labarin cewa mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya raba motoci kirar sharon ga 'yan mazabarsa.
Sanatan ya ce ya raba motocin ne ga wadanda rabonsu ya tsaga domin saukaka musu sufuri daga gida zuwa kasuwa ko ofis ko gonakinsu.
Asali: Legit.ng