Home Back

Gwamna Ya Dakatar da Kwamishina Bayan Gano Wata Baɗaƙala, Ya Ɗauki Mataki

legit.ng 2024/6/26
  • Alex Otti na jihar Abia ya dakatar da kwamishinar lafiya ta jihar, Dr. Ngozi Okoronkwo bisa zargi rashin gaskiya da almundahana
  • Wani jami'in gwamnatin Abia ya bayyana cewa Gwamna Otti ya ɗauki matakin ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan zargin da ake mata
  • Wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnatin Abia ta dakatar da shugabar makarantar jinya bisa zargin aikata ba daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Alex Otti ya dakatar da kwamishinar lafiya ta jihar Abia, Dokta Ngozi Okoronkwo.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya dakatar da ita ne bisa zargin rashin gaskiya da kuma almundahanar makudan kudade.

Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Gwamma Otti na jihar Abia ya dakatar da Dokta Ngozi daga matsayin kwamishinar lafiya Hoto: Alex Otti Asali: Facebook

A rahoton jaridar Vanguard, an dakatar da kwamishinar har sai baba-ta-gani a wurin taron majalisar zartarwa na jihar Abia ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani babban jami’in gwamnatin Abia ya tabbatar wa jaridar cewa da gaske ne gwamnan ya nemi kwamishinar lafiya “ta sauka daga muƙamin ta koma gefe."

A cewar jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa, gwamna ya ɗauƙi matakin ne domin ya bayar da damar gudanar da bincike kan Dr. Ngozi da ma’aikatarta.

Ya ce:

"Akwai ayar tambaya a yanayin gaskiyarta yayin gudanar da ayyukan da ke kanta kuma gwamna na ganin wasu abubuwan sun saɓawa manufarsa ta yin gaskiya da rikon amana.
"Saboda haka ne ya umarci kwamishinan ya sauka domin a gudanar da bincike a tsanake ba tare da samun cikas ba."

A halin da ake ciki dai duk wani kokarin jin ta bakin Kwamishinar ya ci tura domin bata amsa kiran da aka yi mata ta wayar tarho ba, rahoton Naija News.

Dakatar da kwamishinar na zuwa ne sa’o’i 48 bayan dakatar da shugabar makarantar koyon aikin jinya, Abiriba, bisa zargin ta da hannu rashin gaskiya da cin amana.

Gwamna Eno ya tsige kwamishina

Rahoto ya zo cewa Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Eno ya tsige kwamishinan ayyuka na musamman, Bassey Okon daga muƙaminsa, ya umarci ya bar ofis nan take.

Sakataren gwamnatin jihar Akwa Ibom, Prince Enobong Uwah ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024

Asali: Legit.ng

People are also reading