Home Back

Sojoji sun dagargaza Ƴan bindiga da dama a jihar Kaduna

premiumtimesng.com 2024/7/3
Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana walwala na awa 24 a duk faɗin jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Bisa ga takardar Aruwan ya ce rundunar sojin sama da kasa dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Whirl Punch’ ne suka murkushe maharan.

Ya ce dakarun sun samu wannan nasara bayan sun tattaro bayanan sirri kan aiyukan maharan da kuma shirin gudanar da wani taro a cikin dajin.

“Bayan jami’an tsaron sun tabbatar da wurin da maharan za su gudanar da taron shi ne suka Kai wa wurin hari.

“A dalilin haka dakarun suka samu nasarar kashe mahara da dama inda a ciki akwai Alhaji Kachalla Ragas tsohon abokin Buharin daji.

Bayan haka gwamnan jihar Uba Sani ya yaba namijin kokarin da jami’an tsaron suka yi a jihar.

Daga nan sai Kwamishina Aruwan ya hori murane da suka gaggauta sanar da mahukunta irin wasu ayyuka na ƴan bindiga a jihar.

People are also reading