Home Back

Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya Aminu Ado Bayero Miliyan Goma.

dalafmkano.com 2024/7/3

Babbar kotun tarayya mai zaman ta a Gyadi-gyadi karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobida, ta yanke hukunci akan batun karar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya shigar akan batun umarnin da gwamna ya bayar na a kama shi.

Justuce Amobeda ya ayyana cewar kada wata hukuma ta kama Alhaji Aminu Ado Bayero, kuma an ayyana cewar yana da ƴancin ya zagaya duk inda yake a fadin kasar nan.

Kotun ta kuma ayyana cewar gwmnatin jahar Kano ta biya mai karar wato Aminu Ado Bayero, Naira miliyan goma ladan tsoratar da shi da gwamnatin ta yi.

Sai dai lauyan gwamnati Barrista Ibrahim Isah Wan gida, ya bayyanawa wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il cewar, wannan hukunci bai shafi masarautar Kano ba, domin babu inda kotun ta ce abinda majalisa tayi ba dai-dai ba ne, kawai dai an bayyana cewar kada a danne wa mai ƙara hakƙinsa wanda kundin tsarin mulkin ƙasa ya bashi.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewar, yayin zaman shari’ar an girke jami’an tsaro a harabar kotun, domin samar da tsaro a yankin.

People are also reading