Home Back

Sarautar Kano: NNPP ta Tsoma Baki Kan Lamarin, Ta Nemowa Sanusi II da Aminu Ado Mafita

legit.ng 2024/7/5
  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan Sarautar jihar Kano, jam'iyyar NNPP ta tsoma baki kan rikicin a jihar
  • Jam'iyyar ta bukaci duka bangarorin biyu da ke neman kwace kujerar da su yi taka tsan-tsan wurin bin doka da oda
  • Uban jam'iyyar a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jihar Lagos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta yi martan kan rikicin sarautar Kano da ya ki ci ya ki cinyewa.

Jam'iyyar ta bukaci a bi tsarin doka da oda domin warware matsalar sarautar jihar ba tare da matsala ba.

Wanda ya assasa jam'iyyar a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam shi ya bayyana haka a yau Alhamis 30 ga watan Mayu a jihar Lagos, cewar Daily Nigerian.

Aniebonam ya bukaci bin lamarin a hankali domin samar da tsaro cikin jihar ba tare da tayar da hankula da jefa jama'a cikin rudani ba.

"Jihar Kano ce kawai NNPP ke mulka, a matsayin mu na jam'iyya mai son zaman lafiya, mun yarda da bin doka."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kamata mu kula da zaman lafiyar jihar Kano fiye da muradun wasu daidaiku."
"Abin da ya fi muhimmanci a kokarin neman kujerar sarautar jihar shi ne duka bangarorin biyu su tabbatar da bin doka da oda."

- Boniface Aniebonam

Abba Kabir ya gana da nuna Ribadu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gana da mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Abba Kabir ya yi ganwar da Ribadu ne a ofishinsa da ke birnin Abuja a yau Alhamis 30 ga watan Mayu.

Wannan ganawa da zuwa ne bayan zargin Ribadu da hannu a rikicin sarautar jihar Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Asali: Legit.ng

People are also reading