Home Back

Kukah ya ziyarci Tinubu, ya baje masa nau’o’in raɗaɗin ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya ke fama da su

premiumtimesng.com 2024/9/27
Kukah ya ziyarci Tinubu, ya baje masa nau’o’in raɗaɗin ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya ke fama da su

Shugaban Mabiya Ɗariƙar Katolika da ke Sokoto, Mathew Kukah, ya yi kira ga gwamnati ta matsa kusa da jama’a domin ta san hanyar da za ta share masu raɗaɗin ƙuncin tsadar rayuwa da ake fama a faɗin ƙasar nan.

Kukah ya bayyana haka a ranar Laraba, bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.

Kukah ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala ganawar sa cewa, ya shaida wa Tinubu ‘yan Najeriya na gaganiya da fafutikar nau’o’in raɗaɗin tsadar rayuwa daban-daban, waɗanda ya ce duk sun samo asali ne daga wasu tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta bijiro da su.

Ya ce duk da dai shekara ɗaya ba ta isa a aura nagarta ko akasin nagartar gwamnatin Tinubu ba, to duk da haka ya kamata gwamnati ta gaggauta kusantar jama’a domin ta ƙara yi masu bayanin nisan zangon da za a ƙara yi nan gaba, kafin a fita daga cikin wannan matsatsi.

A ranar 29 ga Mayu ne Shugaba Tinubu zai cika shekara ɗaya kan mulki.

“Na tabbatar cewa shekara ɗaya ta yi kusa a ce za a auna nagartar wannan gwamnati. To amma kuma a matsayin da muke ciki a yanzu, mun san cewa muna cikin wani mawuyacin halin da ya yi tsanani sosai.

“Yan Najeriya na fama da matsanancin ƙuncin rayuwa a matakai daban-daban. Kuma ƙunci ne da ba a so shigar da ba. Amma ya faru ne daga wasu tsare-tsaren da gwamnati ta bijiro da su, waɗanda ake fata nan gaba za a gyara domin su yi wa jama’a alfanu.

Kan rikicin siyasar Jihar Ribas kuwa, Kukah ya ce, a rabu da ‘yan siyasa, “saboda idan su na faɗa, sun san yadda za su sasanta junan su. Saboda haka ina fatan nan ba da daɗewa ba Jihar Ribas za ta saisaita, saboda ta na da muhimmanci a Najeriya.”