Mawaƙiya Tyla da zaɓen Murtaniya cikin hotunan Afirka
Zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan Nahiyar a wasu sassa na duniya
A ranar Lahadi, mawaƙiyar Afirka ta Kudu Tyla ta anshi kambun karramawa guda biyu a wajen taron BET da aka yi a Amurka.
A jajibirin zaɓen shugaban ƙasar Mauritaniya, wani mutum ya isa babban masallacin birnin Nouakchott domin yin sallar Juma'a...
Magoya bayan shugaban ƙasar Mauritaniya mai ci na murna bayan sake zaɓarsa da aka.
Sai dai wanda ya zo na biyu ya yi zargin cewa an yi aringizon ƙuru'u.
Rana ta biyu kenan da mayaƙin Najeriya Burna Boy.
Silvio de Sousa na Angola da Willy Hernangomez na Spain sun fafata a wasan neman gurbin shiga gasar kwallon kwando ta Olympics ranar Laraba.
Masinta masu kamun kifi sun fito da abin da suka kama a birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast a ranar Asabar.
Dan tseren keke na kasar Eritrea, Biniam Girmay bayan ya lashe mataki na uku a gasar Tour de France ranar Litinin.
Ya zama baƙar fata na farko a Afirka da ya lashe ɗaya daga cikin matakai 21 na wannan shekarar.
Ƴar wasan golf ta Najeriya, Georgia Oboh a gasar Dow Championship a Amurka.
An ci gaba da zanga-zanga a Kenya a ranar Talata duk da matakin da shugaban ƙsar ya ɗauka na janye dokar da ta ƙunshi ƙarin haraji a ƙasar.
Matasa ne suka jagoranci zanga-zangar a dukkan manyan biranen ƙasar da garuruwan dake faɗin ƙasar.
A ranar Juma'a a birnin Nabeul na ƙasar Tunisia inda wata mata ke baza kuskus cikin rana domin ya bushe.