Bayan Shafe Shekaru 15 a Gidan Yari, Kotu Ta Saki Wani Mutum Ba Tare da Shari'a Ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - A ranar Litini ne babbar kotun jihar Legas dake Ikeja, ta ba da umarni a saki wani mutum mai suna Kazeen Adeshina, bayan kwashe shekaru 15 a gidan yari ba tare da an yi shari'arsa ba.
Mai shari'a Oyindamola Ogala, ya bayar da umarnin sakin mutumin a wani hukunci da ya yanke kan ƙarar take hakkinsa na ɗan Adam da aka yi ta hannun lauyansa Ben Okeke.
Premium Times ta bayyana cewa, alƙalin yace ajiye Adeshina a gidan yari ba tare da laifi ko shari'a ba rashin adalci ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Ogala ya ce babu adalci a kama Adeshina da cigaba da tsare shi da aka yi a gidan gyaran hali na Kirikiri da ke Legas ba tare da gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Bayan duba shari'ar Adeshina, alƙalin ya bayar da umarnin sakin Adeshina nan take kuma ba tare da cika wasu sharuɗɗa ba, kamar yadda jaridar Guardian ta bayyana.
A ruwayar Vanguard, Lauyan Adeshina, Mista Okeke, ya yi karar Antoni Janar na Legas, kwamishinan 'yan sanda, shugaban hukumar gidan gyaran hali da gwamnatin Legas.
Mista Okeke ya roki kotun da ta bi wa wanda yake karewa kadin tauye hakkinsa na dan Adam da aka yi sakamakon tsare shi na tsawon shekaru 15 ba tare da shari'a ba.
A wani labari na daban, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya saka rigar Naira miliyan uku inda ya halarci wani taro.
Cike da fushin halin da talakawa suke ciki, 'yan Najeriya sun yi masa tatas bayan bayyanarsa da rigar mai nuna aji da isa.
Asali: Legit.ng