Home Back

Za a binciki yadda NNPC ya shigo da gurɓataccen fetur da lalataccen iskar gas

premiumtimesng.com 2 days ago
Gwamnati ba ta kara farashin litar mai ba – Minista Sylva

Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin sanata 15 waɗanda za su binciko ya aka yi har aka shigo da gurɓataccen fetur da ruɓaɓɓen gas masu illa a ƙarƙashin NNPCL.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a lokacin da yake naɗa kwamitin a zaman Majalisar Dattawa na ranar Laraba.

Ya ce Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ne zai shugabanci kwamitin.

Sauran mambobin sun haɗa da Sanata Asuquo Ekpenyong, Abdullahi Yahaya, Tahir Monguno, Olamilekan Adeola, Diket Plang, Abdul Ningi, Khabeeb Mustapha, Ipanibo Banigo, Adams Oshiomhole, Adetokunbo Abiru, Osita Izunaso, Sahabi Ya’u, Olajide Ipinsagba da Ekong Sampson.

Zartas da shawarar yin binciken gano yadda aka shigo da gurɓataccen fetur da gas ɗin ya zo ne bayan Sanata Ekpeyong ya gabatar da ƙorafin hakan.

Ekpeyong ya yi ƙorafin cewa akwai tsananin damuwa dangane da yadda ake shigo da gurɓataccen mai a cikin Najeriya.

Sanatan ya ce gingima-gingiman jiragen ruwa 12 ne suka dangana da tashoshin ruwan Lome a Togo da kuma Najeriya da wasu ƙasashen Afrika ta Yamma, a ranar 16 ga Yuni.

Ya ce fetur ɗin da suka sauke ba shi da inganci, amma a haka ake ci gaba da sayar da shi a gidajen mai.

Ya ce an sauke man a Lome daga nan aka loda wa wasu jiragen waɗanda suka yi dakon sa zuwa tashar jiragen ruwa ta Warri, Najeriya, a ranar 21 ga Yuni, 2024.

Ya yi gargaɗin a guji gurɓataccen fetur, kuma a haramta shigo da fetur daga jigari-jigarin kamfanin tace ɗanyen mai.

Shi ma Sanata Ndume ya yi gargaɗin cewa Najeriya na shigo da gurɓataccen fetur daga Rasha, alhali kuma ga fetur a nan Najeriya masana’antar cikin gida na tacewa.

People are also reading