Home Back

NDIC: Gwamnati ta yi Gwanjon Dukiyar Bankin Heritage da CBN Ya Karbewa Lasisi

legit.ng 2024/7/6
  • Hukumar kula da kudin masu ajiya a bankuna (NDIC) ta bayyana cewa ta sanya kayan bankin Heritage a kasuwa bayan durkushewa da bankin ya yi wanda ya sa ya daina aiki
  • Za a yi gwanjon kayan da ke babban ofishinsa a Legas a lamba 143 da ke titin Ahmadu Bello, Victoria Island inda za a sayar da motoci, ginin da wasu injina, sai kuma na ofishin Ribas
  • Manajan Daraktan NDIC, Bello Hassan a makon da ya gabata ne ya bayyanawa 'yan Najeriya cewa bankin ya durkushe kuma za a biya wadanda su ka ajiye akalla N5m ko kasa da haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar da ke kula da kudin masu ajiya a bankuna (NDIC) ta sanya bankin Heritage da sauran rassansa a sassan kasar nan a kasuwa a matsayinta na mai gwanjon bankin.

Daga cikin kayan da hukumar NDIC ta sanya a kasuwa akwai motoci, wasu kayan ofis, shuke-shuke, injina da wasu kayayyaki a rassa 62 na bankin da ke fadin Najeriya.

Hukumar NDIC
NDIC ta fara gwanjon kayan bankin Heritage Hoto: Nigeria Deposit Insurance Corporation - NDIC Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa hukumar NDIC ta gayyaci jama’a su bi hanyar da ta dace wajen sayen kayyyakin, inda za a zabi wadanda su ka cancanta a sayar masu da kayan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sayar da kayan bankin Heritage

Hukumar NDIC ta bayyana cewa za ta cefanar da kayan bankin Heritage inda za a karbi la’adar kaso 10% daga wanda zai sayi kayayyakin da suka rage a bankin ga wadanda ke bukata.

Za a sayar da kayan bankin da ke babban ofishinsa a Legas a lamba 143, titin Ahmadu Bello, Victoria Island inda aka saka injin samar da wuta, ginin bankin da motocin bankin a kasuwa.

Haka kuma za a sayar da wasu kayan bankin a rassansa hudu da ke babban birnin tarayya Abuja, wasu rassa hudu a jihar Ribas da sauran jihohin kasar nan.

A baya, hukumar NDIC ta bayyana cewa ta fara tantancewa tare da biyan wadanda su ka ajiye kudinsu da ya kai N5m ko kasa da haka wanda su ne 99% na abokan huldar bankin, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Manajan Daraktan NDIC, Bello Hassan ya bayyana a wata hira da manema labarai cewa bankin Heritage ya durkushe, kuma akalla akwai kudin jama’a N650bn ajiye a asusunsu na bankin.

NDIC za ta fara biyan kwastomomi

A baya mun kawo mu ku labarin cewa hukumar kula harkokin kudin ajiya a bankunan kasuwanci (NDIC) ta bayyana cewa za ta fara biyan abokan huldar bankuna 154 da aka lasisinsu.

Babban bankin kasa na CBN ya kwace lasisin bankunan a shekarar 2018, kamar yadda shugaban hukumar Umaru Ibrahim ya fada, ya ce su na biyan abokan huldar kananan bankuna kudinsu.

Asali: Legit.ng

People are also reading