Home Back

JANYE TAKUNKUMI: Tinubu ya umarci ECOWAS ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar, Burkina Faso, Mali

premiumtimesng.com 2024/4/29
JANYE TAKUNKUMI: Tinubu ya umarci ECOWAS ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar, Burkina Faso, Mali

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ECOWAS da ta janye takunkumin karya tattalin arziki da ta kakabawa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

Kungiyar ECOWAS ta kakaba takunkumin ne biyo bayan sauye-sauyen da aka samu na gwamnati a kasashen yammacin Afirka a lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a kasashen.

Tinubu, ya ce takunkumin bai yi tasiri ba kuma bashi da amfani a yanzu.

” Na ɗauka wannan takunkumi da muka saka zai tilasta shugabannin da suka yi juyin mulki su dawo teburin shawara, a tattauna don samun matsaya, amma kuma sai ya zama ƙaya, ba ta yi amfani ba sannan ba a yi nasara ba.

” Ganin cewa ba a samu yadda ake so ba dole, kuma akwai matsaloli da dama da suka taso sannan ta tattaunawa da ake yi game da halin da waɗannan kasashe suka shiga tun bayan kakaba musu takunkumin, na yi kira ga ECOWAS da ta janye takunkumin.

” Sannan kuma gashi a halin yanzu mun tunkari watan ramadan da ke tafe, da kuma azumi da kiristoci suka fara domin Ista. Hakan ya sa muka ga ya dace ECOWAS ta janye takunkumin domin a samu walwala.

 
People are also reading