Home Back

Shugabar IMF: Kokarin Zurfafa Gyare-gyare A Kasar Sin Zai Haifar Da Karin Ci Gaban Tattalin Arzikinta

leadership.ng 2024/6/29
Shugabar IMF: Kokarin Zurfafa Gyare-gyare A Kasar Sin Zai Haifar Da Karin Ci Gaban Tattalin Arzikinta

Wakilin CMG ya zanta da shugabar Asusun Lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva a kwanan baya, inda ta bayyana cewa, manufar gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje da aka aiwatar a kasar Sin cikin shekaru 40 da suka wuce, ta haifar da dimbin alfanu ga al’ummar kasar. 

A cewarta, yanayin da tattalin arzikin Sin ke ciki ya sauya daga mai samun karuwa cikin matukar sauri, zuwa na tabbatar da ingancin ci gaban da aka samu, wanda ya sa shugabannin kasar daukar matakan zurfafa gyare-gyaren da ake yi, ta yadda za a samar da karin damammaki na bunkasa tattalin arziki a kasar ta Sin.

Sa’an nan, a lokacin da ta ambaci matakin kasar Sin na raya sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, Georgieva ta ce, don samar da karin karfin bunkasa tattalin arziki, ya kamata a rungumi kimiyya da fasaha, da zuba jari a fannin horar da ma’aikata. A wannan fanni, a cewarta, kasar Sin tana kan gaba a duniya.

Ban da haka, Malama Georgieva ta ce, nasarar da kasar Sin ta cimma ta shafi yadda aka kyautata zaman rayuwar jama’a, da baiwa daukacin al’ummar kasar damammaki na more ci gaban da kasar ta samu. Asusun IMF, da Bankin Duniya da ta taba aiki da su, dukkansu suna kokarin raba fasahohin kasar Sin a sassa daban daban na duniya, da zummar mai da nagartattun dabaru na Sin ilimi, da nasarori na mabambantan kasashe. (Bello Wang)

People are also reading