Home Back

An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sojoji a Shingen Bincike

legit.ng 2024/9/27

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Ana fargabar ƴan bindiga sun kashe sojoji uku na rundunar birged 14 ta sojojin Najeriya da ke Ohafia a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun hallaka sojojin ne waɗanda ke aiki da bataliya ta 144 a garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar Abia.

'Yan bindiga sun farmaki sojoji a Abia
'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Abia Hoto: HQ Nigerian Army Asali: Facebook

An kashe sojojin ne a wajen shingen binciken sojojin da ke kan kwanar Obikabia kusa da Umuola a ƙaramar hukumar Aba ta Arewa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Ƴan bindigan waɗanda suka rufe fuskokinsu, sun zo ne cikin wata mota baƙa ƙirar SUV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun shammaci sojojin ne waɗanda suke bakin aiki lokacin da suka kai musu harin.

An tattaro cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da bindigun sojojin.

Sun kuma ƙona motar sintirin da jami’an tsaron ke amfani da ita da shingen binciken kafin su tafi.

Asali: Legit.ng

People are also reading